<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><author>Wade, John Francis (circa 1710-1786), Hillsong Worship</author>
<hymn_number>74</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Mu zo duk mutane, amintattu na Allah,
 Yau cikin Baitalahmi, Mai Ceto ya zo.
 Tauraron gabas, tauraron asubahi,
 Mu kawo masa yabo, mu kawo masa ƙauna.
 Mu shaida nasa suna, Immanuel.

[V2]
 2) Ga shi, marar iko, da jiki na ƙanƙanci!
 Duba! ya ɗauki dukan tabi'armu!
 Hasken mutane! Hasken dukan duniya!
 Mu zo da kayan ƙanshi, mu zo mu rera waƙa,
 Mu zo, mu yabi Yesu Immanuel.

[V3]
 3) Alhamdu ga Yesu ! Ya Yesu, mun gaishe ka!
 Muna sujadarmu gare ka a yau.
 Kalmatu 'Llahi! Bayyanuwar Mai Iko!
 Mu ɗaukaka sunanka, mu yi maka sujada
 Mu ba ka duk sarauta, Immanuel.</lyrics>
<title>Mu Zo Duk Mutane, Amintattu na Allah LW74</title>
</song>